ABNA24: Muhammad Samsar jakadan kasar Turkiya a Rasha ya fadawa kamfanin dillancin labaran Tas na kasar Rasha a jiya Laraba kan cewa turkiya ta sayi garkuwan makaman kan dalar Amurka biliyon biyu da rabi, kuma tuni ta karbi garkuwa na farko a shekara ta 2019 sannan nan ba da dadewa ba zata karbi dayan daga kasar ta Rasha.
Kasar Turkiya ce kasa, mamba a kungiyar tsaro ta NATO wacce ta sayi irin wannan garkuwan makamai masu linzami daga kasar Rasha.
Gwamnatin Amurka ta dorawa kasar ta Turkiya takunkuman tattalin arzikin kan wannan cinikin, sannan ta fasa sayarwa kasar Turkiya jiragen yaki samfurin F-15 kirar Amurka.
342/